Russian ambassador shot in Ankara, Turkey

Russian Foreign Ministry confirmed that Russian ambassador to Turkey was shot and “seriously wounded” after a gunman stormed into a building where the official was attending a Russian photo exhibition.


“Wani wanda ba a san ko wanene ba ne ya bude wuta a yayin wani taron jama’a a Ankara. Sakamakon haka, jakadan Rasha a Turkiyya ya samu raunin harbin bindiga,” mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Rasha Maria Zakharova ta shaida wa manema labarai.

Bisa sabon bayanin da ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta fitar, yanzu haka ana jinyar Karlov a nan take kuma ba a kai shi wani asibiti ba, kamar yadda aka ruwaito a baya.

Jakadan, Andrey Karlov, ya ji rauni bayan da yake shirin gabatar da jawabi kan bude baje kolin "Rasha a idon Turkawa."

Hotunan da ake zargin wanda ya aikata laifin dauke da makami na kara yawo a shafukan sada zumunta. Masu amfani da su kuma suna yada hotuna da suka ce sun nuna jakadan Rasha a kwance bayan an harbe shi.

Wanda ya aikata laifin, wanda ke sanye da kwat da tie, ya yi ihun ‘Allahu Akbar’ (‘Allah ya kyauta’ a Larabci) a lokacin harin, kamar yadda kafar yada labarai ta AP ta rawaito, inda ta ambato mai daukar hoton nasu.

Har ila yau maharin ya fadi kalmomi da dama cikin harshen Rashanci, kamar yadda kamfanin dillancin labarai ya bayyana, ya kuma lalata da dama daga cikin hotuna a wurin baje kolin.

Tashar talabijin ta NTV ta Turkiyya ta ce an kuma jikkata wasu mutane uku a harin da aka kai wa jakadan.

Kamfanin dillancin labaran Anadolu ya bayar da rahoton cewa, dakarun Turkiyya na musamman ne suka kashe maharin. Interfax ta Rasha, ta nakalto majiyar rundunar sojin Turkiyya, ta kuma tabbatar da cewa an kashe dan bindigar.

Jaridar Hurriyet, ta nakalto dan jaridar nasu, ta ce wanda ya aikata wannan aika-aika ya kuma yi harbin gargadi a iska kafin ya auka wa Karlov.

A cewar jaridar, dakaru na musamman sun kewaye ginin da aka kai harin inda suke neman dan bindigar.

Shaidu sun ce ‘yan sanda sun yi artabu da maharin.

Leave a Comment